Jihar Bauchi zata samu makarantar koyon Sarrafa danyen man Fetur da iskan gas.


Komishinan ma'adanai na

Jihar Bauchi Nuruddeen

yayi wani babban abin bajin ta da ya samo ma Arewa mafita a taron fadada tattalin arzikin Najeriya.


Gwamnatin tarayya ta shirya taron  fadada tattalin arzikin Najeriya domin rage dogaro da danyen Man fetur zuwa sinadarin iskan gas duba da tsadan farashin man a kasuwannin duniya tare da gurbata muhalli wadda hakan yakan janyo koma baya wajen aiwatar da kasafin kudin kasa,


Hukumar gudanarwa ta Gwamnatin tarayya Kan Ma'adanan danyen Man Fetur  ta Kasa ta shirya bita Karo na biyar Mai taken: " Karfin  arzikin iskan gas a Nigeria, tare da yadda za'a habaka shi wadda ya gudana daga Ranar 23 zuwa 26 ga watan nuwamba 2020  a Yenagoan Jihar Bayelsa.


Taron wanda yasamu halartan masu ruwa da tsaki a sassa dabam-dabam na Kasar Nan,


Jihar Bauchi ta samu wakilcin Komishinan dake jagorantar Hukumar ma'adanai na kasa Hon. Nuruddeen Abdulhameed.


Yayin Gudanar da taron Mal. Nuruddeen ya gabatar da manyan kudurori guda biyu da suka ja hankali a taron kuma suna da alaka chigaban jihar Bauchi da Arewacin Nijeriya baki daya.


Ga kuduran da ya gabatar - :


Komishinan ya gabatar da kuduri kamar haka


(1) Bukatar dake akwai a halin yanzu na cewa wajibi ne hukumar (NNPC) ta tabbatar da kirkirar Makarantar koyon aikin sarrafa Man-fetur a Karamar Hukumar Alkaleri dake Jihar Bauchi wanda kamfanin NNPC take aikin hakar mai a halin yanzu. Wanda wannan Qudiri yanzu Alhamdulillahi ya samu karuwa a wajen taron. 


 (2) kuduri na biyu da komishinan ya gabatar - :


Komishinan ya nemi a Sanya Jihar Bauchi dama dukkan jihohi masu arzikin iskar Gas dake shi'ar arewa maso Gabashin Nigeria cikin dukkan shirye-shiryen Gwamnatin tarayya akan ciyar da sinadarin iskan Gas gaba,  sannan Kuma a shigar dasu cikin aikin Samar da hasken wutan lantarki ta hanyar amfani da iskan gas daga garin Ajaokuta-Kaduna Zuwa Kano (AKK).


Abin ban sha'awa-:

Wadannan kudurori  da Komishinan ma'adanai na Jihar Bauchin ya gabatar na daga cikin Kuduri da suka ja hankali Sosai tare da haifar da zazzafan muhawara, wadda daga karshe Suka samu amincewar taron majalisar gabadaya,


Wadda hakan ke nuni dacewa kenan Jihar Bauchi zata zamto jiha ta biyu a kasa Baki Daya da zata mallaki Makarantar koyon Sarrafa danyen man Fetur da iskan gas bayan Jihar Delta,


A halin yanzu a mataimakin jiha-:.


Mai girma Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed cike da farin ciki da wannan cigaba da komishinan ya kawo. Take Gwamnan ya aike da kudirin zuwa majalisar jiha domin samun amincewar  Yan'majalisun jihar yanda kai tsaye suka amince baki-daya. Ganin babban abin alherin da aka zo da shi. 


Cikin wanda suka samu halartan taron a Yenagoan Jihar Bayelsa.


Sun hada da: Mataimakin Gwamnan Jihar Bayelsa Sen. Lawrence Ewhrudjakpo,  da kuma sakataren Din-Din-Din a Hukumar kula da Danyen man Fetur ta kasa Mr. Bittus B Nabasu tare Kuma da Babban Sakatare Hukumar kula da daidaitob kasabta kudin danyen Man fetur (PEFMB) Ahmad a Bobboi, tare da Manyan Hukumomi masu ruwa da tsaki wajen Sarrafa Danyen Mai ta Kasa.


Rahoton Geo-Barrister,

29-Nov-2020.

Comments